You are using an outdated browser. Please upgrade your browser to improve your experience.
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

by Abdulkarim Nasir
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

What is it about?

Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar

App Details

Version
1.1
Rating
(2)
Size
151Mb
Genre
Education Lifestyle
Last updated
October 12, 2019
Release date
June 11, 2019
More info

App Screenshots

Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar screenshot-0
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar screenshot-1
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar screenshot-2
Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar screenshot-3

App Store Description

Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam

Download this app to learn how to pray the Muslim Prayer as taught by Prophet Muhammad (s.a.w). The audio is in Hausa language and works perfectly offline.

1. BABU TALLA WATO (No-Ads) ACIKIN WANNAN MANHAJJA
2. APP YANA AIKI BA TARE DA ANKUNNA DATA BA

Aciki Siffatus Salatin Nabi mp3 zakuji karatun littafin (Sifat Salat Nabiy Hausa) a inda mawallafin littafin Muhammad Nasirudden Al Albani yayi bayanin yadda sallar manzon Allah (s.a.w) take tun daga kabbarar-harama zuwa sallama kamar kana Kallon Annabi yanayin sallar. Fassarar littafin da darusan na marigayi mallam Jafar Mahmud Adam ne.

Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 Offline

Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.

Tun kafin zuwansu Kano, marigayi Sheikh Ja'afar yariga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma
Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan.

Kana, kafin rasuwarsa, ya riga yayi nisa wajen karatunsa na digiri na 3, wato digirin digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).

Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya bar mata 2, da 'yaya 6, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.

Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.

Disclaimer:
AppAdvice does not own this application and only provides images and links contained in the iTunes Search API, to help our users find the best apps to download. If you are the developer of this app and would like your information removed, please send a request to takedown@appadvice.com and your information will be removed.